Hukumar yan sanda ta mayar da martani ga Danjuma Goje, tace tantirin makaryaci ne

Hukumar yan sanda ta mayar da martani ga Danjuma Goje, tace tantirin makaryaci ne

-Hukumar yan sanda ta mayar da sakon kar ta kwana ga Sanata Danjuma Goje

- Tace sanatan tantirin makaryaci ne

Hukumar yan sandan Najeriya tayi raddi ga tsohon gwamnan jihar Gombe, kuma sanata Abdullahi Danjuma Goje, akan maganar cewa hukumar ta sace kasafin kudin 2017.

Kwanakin baya hukumar yan sanda sun kai hari gidan sanatan inda suka kwashi wadansu abubuwa da dama.

A wata jawabi Danjuma Goje yayi a filin majalisar dattawa ranan Laraba, sanatan yace yan sanda sun kwace kudi N18m daga hannun mazauna gidan guda 50, kuma sun dauke masa na’ uara Komfuta da kuma takardu 18 wada kasafin kudin kasa na ciki.

Kasafin kudin 2017 : Hukumar yan sanda ta mayar da martani ga Danjuma Goje, tace tantirin makaryaci ne

Danjuma Goje tantirin makaryaci ne

Raddi akan hakan, hukumar yan sanda ta saki wani jawabi a daren laraba inda tace wannan magana tasa zuki ta malle ce.

Kakakin hukumar, Jimoh Ibrahim yace : “ Wannan magana karya ce gaba dayan ta kuma kokarin juya hankalin yan Najeriya ne.

“Ya kamata yan Najeriya su sani cewa hukumar yan sanda ta samu izini daga kotu cewa tayi binciken gidan Danjuma Goje a ranan 20 ga watan Afrilu da ke No. 10 Haile Salasie Street, Asokoro District Abuja, bayan ta samu rahoton cewa akwai wani kudin haram da takardu a gidan.

KU KARANTA: Amurka tayi raddi ga Goodluck Jonathan

“Ku sani cewa lokacin da jami’an yan sanda suka isa gidan Sanata Danjuma Goje, mai kula da gidan Ango usman ya kira Sanatan ya fada masa abinda ke faruwa kuma sanatan yayi alkawarin cewa zai zo, amma daga baya sai ya kashe wayansa.

“An gudanar da binciken a gaban makusantan Sanata Danjuma Gojen guda 3 wadanda ke zama a gidan.

Yan uwan nasa guda 3 sun kaimu wurare daban-daban cikin gidan kuma sun rattaba hannayensu bayan binciken inda muka dauko kudade, takardu, Komfuta, kuma babu kasafin kudin 2017 a ciki.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel