Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya game da Sarki Sanusi da masarautar sa

Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya game da Sarki Sanusi da masarautar sa

- A baya bayan nan ne hukumar EFCC ta yi yunkurin binciken masarautar Kano bisa zargin cewa an yi faccaka da kudade har Naira miliyan dubu hudu

- Kanawa da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu, kowana lungu da sako mutane ke taruwa a jihar ta Kano, fadin badakala da ta kunno kai a masarautar Kano suke yi, kamar yadda majiyar mu ta rawaito

Wani Ibrahim Abdullahi yace tarihi ne ke maimaita kansa saboda sarkin yanzu Muhammad Sanusi ll ba mutum mai tsoro ba ne, ya gaji kakansa sarki Sanusi na daya kuma shi mutum ne mai tsayawa kan gaskiya.

Yayinda Umar Ibrahim Usman ke cewa yana goyon bayan gwamnati ta binciki lamarin saboda faccaka tayi yawa a Najeriya, don haka ya kamata a tabbatar da gaskiyar lamarin

NAIJ.com ta tsinkayi shi kuma Umar Abdulwahid yace ana hangen masarauta tana da laifi ai gwamnati ma tana da laifi, yace idan an taba masarauta shi ba zai ji dadi ba saboda an ga sarki na taimakawa jama’a sun soma adawa dashi domin su tsige shi.

Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya game da Sarki Sanusi da masarautar sa

Mabambantan ra'ayoyi na ci gaba da kwaranya game da Sarki Sanusi da masarautar sa

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta sake gayyatar Babachir

Gwamnatin tarayya da tace zata taimaka masu bata yi ba amma tana son ta binciki mai taimako, yace bayin Allah mata da goyo da ‘ya’yansu da dama masarautar kano ke matukar taimakawa amma duk ba a gani.

Dr. Musa masanin kimiyar zamantakewa ne kuma yayi sharhi akan harkokin da suka safi mulkin fada, yace masarauta tana da wani matsayi akan zukatan al’umma shi ya sa ana ganin sarki uban kowa ne. Ana ganin yana da wani iko na tafiyar da kudaden dake tare dashi ba tare da tilas ya fiti ya yiwa ‘ya’yansa bayani ba..Yace kowa ya kamata ya ja kimarsa, ya ja darajarsa.

Masarauta ta ja kimarta ta rufe kofofin da ta bude da suka sa ake kawo mata farmaki, Gwamnati kuma ya kamata ta gane taba masarauta tamkar taba darajar sarkin dake kan karagar mulki ne. Taba masarauta na daidai da taba mutuncin al’umma.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon sarkin Kano

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel