‘Yan Najeriya ne sukayi zabe’ – Amurka tayi raddi ga Jonathan

‘Yan Najeriya ne sukayi zabe’ – Amurka tayi raddi ga Jonathan

-Kasar Amurka tayi magana kan zargin da Jonathan yayiwa Obama

-Ta mayar da martani ne ta ofishin jakadancinta a Najeriya

Kasar Amurka tayi raddi ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, inda suka jaddada cewa ra’ayin yan Najeriya ne ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari nasara a zaben 2015.

Kasar Amurka ta bayyana wannan ne lokacin da yayi mayar da martani akan zargin da Jonathan yayi cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ne yayi sanadiyar faduwarsa zabe.

KU KARANTA: Farfesa Attahiru Jega yayi raddi ga Jonathan

A raddin, kakakin ofishin jakadancin Amurka, Russel Brooks, yace abinda Amurka tayi kawai shine tabbatar da cewa anyi zaben gaskiya.

“Amurka ta bukaci ayi zaben gaskiya ne kawai. Sakamakon zaben ya nuna abinda yan Najeriya ke so,” Brook yace.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel