Shahararen dan wasan Bollywood Vinod Khanna ya rasu yana da shekaru 70

Shahararen dan wasan Bollywood Vinod Khanna ya rasu yana da shekaru 70

- Fitaccen dan wasan Bollywood Vinod Khanna ya rasu

- Khanna wadda ya shahara sakamakon rawar da ya taka a Amar Akbar Anthony ya rasu yana da shekaru 70 bayan yayi fama da cutar daji

- Ya kuma kasance dan majalisa a arewacin yankin Punjab

Fitaccen dan wasan Indiya Vinod Khanna wanda ya fito a fina-finan Bollywood da dama wanda suka hada da Amar Akbar Anthony da Mere Apne ya rasu.

Ya rasu a ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu bayan yayi fama da cutar daji na mafitsara a asibitin Mumbai.

NAIJ.com ta tattaro cewa an kwantar da Mista Khanna wanda ke harkar siyasa ya yi fama da ciwon daji, inda aka kai shi asibiti a farkon wannan watan bayan da rashin lafiyarsa ta yi tsanani.

Shahararen dan wasan Bollywood Vinod Khanna ya rasu yana da shekaru 70

Shahararen dan wasan Bollywood Vinod Khanna ya rasu yana da shekaru 70

An zabe shi zuwa majalisar dokokin kasar sau hudu kuma ya taba zama mataimakin ministan harkokin waje.

KU KARANTA KUMA: Yadda El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Mista Khanna ya fara harkar fim a shekarar 1968 kuma sanan ne ne a Indiya musamman ma a shekarun 1970 da 1980 lokacin da ya yi wasu shahararrun fina-finai.

Mutane da dama na alhinin rasuwar Mista Khanna wanda ya mutu bayan rashin lafiya mai tsanani.

Shugaban Indiya, Pranab Mukherjee ya jagoranci 'yan siyasa da suka nuna jinjina kan rawar da Mista Khanna ya taka a fanin siyasa.

Yayin da wasu fitattun 'yan wasan Bollywood kuma ke nuna alhininsu ga mamacin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kasuwa na bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel