Tattalin arziki: An bayyana lokacin da Najeriya za ta murmure

Tattalin arziki: An bayyana lokacin da Najeriya za ta murmure

– Babban bankin kasar nan ya bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga matsi

– Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki

– CBN ke cewa zuwa tsakiyar shekarar bana abubuwa za su mike

Babban bankin kasar nan watau CBN ya bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga cikin matsi.

Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya bayyana haka kamar yadda mu ka samu labari.

Tattalin arziki: An bayyana lokacin da Najeriya za ta murmure

Tattalin arzikin Najeriya ya ja baya

NAIJ.com na jin cewa Godwin Emefiele ya tabbatar da lallai tattalin arzikin Najeriya zai mike daga karshen rabin wannan shekara. A bisa harsashen bankin na CBN zuwa watan Yuni dai Najeriya za ta samu fitowa daga durkushewar tattali.

KU KARANTA: Attahiru Jega yayi wa Jonathan raddi

Tattalin arziki: An bayyana lokacin da Najeriya za ta murmure

Najeriya za ta murmure kwanan nan-CBN

Gwamnan babban bankin kasar ya bayyana irin kokarin da CBN ke yi na tsagaita tashin Dala. Dalar Amurka ta sauka daga kusan N520 zuwa N370 a cikin ‘yan kwanakin nan. Majalisar Dattawa dai tace ta gamsu da CBN din.

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana cewa gaskiya fa shekaru 8 ba za su isa a gyara Najeriya. Oyegun yace ya zama dole shugaba Muhammadu Buhari yayi tazarce idan har ana bukatar abubuwa su dawo daidai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari ya fitar da Najeriya daga kangin tattali?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel