Abin mamaki: Kungiyar tsoffin manyan ma'aikata da gwamnatin Adamawa sun shiga takunsaka

Abin mamaki: Kungiyar tsoffin manyan ma'aikata da gwamnatin Adamawa sun shiga takunsaka

- Gwamnatin jihar Adamawa na nuna halin ko-in-kula game da halin da suke ciki

- Tsoffin ma’aikata na bin gwamnatin jihar albashin kudaden sallama sama da biliyan N19

- Kungiyar ba ta anfana daga tallafin da gwamnati tarayya ke rabawa jihohi

- Bai kamata gwamnatin dake tutiyar kawo canji,ta mance dasu ba

Tsoffin sakatarorin ma'aikatun gwamnatin Adamawa da gwamnati mai ci a yanzu, sun shiga takun-saka bisa ga rashin biyansu kudaden fansho duk da taimakon da jihar ta samu daga gwamnatin tarayya.

Kungiyar tsoffin manyan sakatarori wato permanent secretaries da ta kunshi akawun majalisar dokokin jihar da tsoffin cif joji da mai binciken kudi dama wadanda ke karbar dunkullelen albashi, na kokawa ne da cewa gwamnatin jihar na nuna halin ko-in-kula game da halin da suke ciki a yanzu na rashin biyansu hakkokinsu na barin aiki.

KU KARANTA: Kasafin kudin 2017 : Hukumar yan sanda ta mayar da martani ga Danjuma Goje, tace tantirin makaryaci ne

Kamar yadda alkalumman kungiyar tsoffin ma’aikata a jihar ke nunawa a jihar Adamawa a.

NAIJ.com ya samu rahoto cewa, shugaban kungiyar tsoffin manyan sakatarorin, Mustapha Galadima ya shedawa taron manema labarai a Yola fadar jihar cewa kungiyar ba ta anfana ko da kwandala ba daga tallafin da gwamnati tarayya ke rabawa jihohi na kudin "bail out" ko kuma Paris Club kamar yadda ake mai lakabi.

A jihar Adamawa tsoffin ma’aikata na bin gwamnatin jihar albashin kudaden sallama sama da biliyan N19

A jihar Adamawa tsoffin ma’aikata na bin gwamnatin jihar albashin kudaden sallama sama da biliyan N19

Shima wani tsohon sakataren dindin din, Alh. Abubakar Hassan ya ce bai kamata gwamnatin dake tutiyar kawo canji,ta mance dasu ba.

KU KARANTA: Shekarar bana: Har yanzu babu kasafin kudi a Najeriya

Kamar Abubakar Hassan shima Mr Emmanuel Vinjir da ya shafe shekara da shekaru yana bautawa gwamnatin jihar yace suma suna da hakki.

To sai dai kuma, gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan yada labaranta Ahmad Sajo ta ce ba haka zancen yake ba.

A cewar kwamishinan, yanzu haka suna aikin tantance tsoffin ma'aikatan domin ganin wadanda suka cancanta su ci gajiyar kudaden sun samu hakkokinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na nuna wata mace da aka gani a Jihar Kwara tana aiki a matsayin 'vulcanizer'

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel