Lafiyar Buhari ba kalubale bane – Gwamnonin APC

Lafiyar Buhari ba kalubale bane – Gwamnonin APC

- Sashin gwamnonin jam’iyyar All Progresives Congress (APC) sun bayyana cewa rashin halartan shugaban kasa Buhari taron majalisar zartarwa karo na uku kan lafiyarsa ba kalubale bane ga kungiyar

- Malam Nasir El-Rufai, wadda ya yi magana a madadin sauran gwamnoni, ya ce ba sabon abu bane don shugaban kasa ya samu wata rashin lafiya

-Ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da yima shugaba Buhari addu’a

Sashin gwamnonin jam’iyyar All Progresives Congress (APC) sun bayyana cewa rashin halartan shugaban kasa Buhari taron majalisar zartarwa karo na uku kan lafiyarsa ba kalubale bane ga kungiyar, cewa basu damu ba kamar yadda ba dole bane sai shugaban kasa ya halarci irin wannan taron.

NAIJ.com ta rahoto cewa da yake jawabi ga manema labarai a daren ranar Laraba bayan wani ganawar sirri tare da kwamitin ma’aikata na jam’iyya mai ci, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wadda ya yi magana a madadin sauran gwamnoni, ya ce ba sabon abu bane don shugaban kasa ya samu wata rashin lafiya a matsayin sa na mai shekaru 74.

Da aka tambaye shi ko gwamnonin jam’iyyar APC da jam’iyyar baki daya na cikin damuwa kan rashin jagorantar taron majalisar zartarwa da shugaba Buhari bai yi ba, El-Rufai ya amsa da a’a.

Lafiyar Buhari ba kalubale bane – Gwamnonin APC

Lafiyar Buhari ba kalubale bane inji Gwamnonin APC

“Bamu damu ba ko kadan a kan al’amarin, ba dole bane sai shugaban kasa ya jagoranci taron majalisar zartarwa. Shiyasa kundin tsarin mulkin mu ya tanadi mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Majalisar wakilai ta ba yan sanda sa’oi 24 su dawo da takardun kasafin kudi

“Shekarun shugaban kasa 74; a wannan shekaru, akwai yiwuwar ya samu wani rashin lafiya, ko ni da nake da shekaru 57 ina ganin likita na rashin lafiya. Addu’an mu shine shugaban kasa ya samu lafiya amma dalilin da yasa aka tanadi mataimakin shugaban kasa, ya kasance saboda irin wannan lokuta, ba lallai bane ya kasance a dalilin rashin lafiya ne ya ki halartan taron, babu mamaki yana da wasu abubuwa da yake gudanar wa. Ba dukka taron majalisar jihar Kaduna nake jagoranta ba saboda mataimakin gwamna na nan idan ina da wasu muhimman abubuwa da zan gudanar.

“Bamu damu ba har yanzu kuma babu dalilin da zai sa mu damu amma ina kira gay an Najeriya da suyi addu’an samun Karin lafiya ga shugaban kasa. An samu ci gaba tun bayan da ya dawo sannan kuma zamu ci gaba da addu’an samun lafiyar sa."

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai yan Kwadago ne ke yin zanga-zanga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel