Hukumar raya tattalin arzikin Arewa maso gabashin Najeriya

Hukumar raya tattalin arzikin Arewa maso gabashin Najeriya

- Jigogin jam’iyyar APC mai mulki sun bada tabbacin fara aikin kafuwar hukumar kula da arewa maso gabas

- Malam Ibrahim Gabanni ya ce hukumar za ta yi nasara ne kawai idan har ta taimakawa matasa su daina bara ko gararanba kan tituna

Yayin da ake sa ran kafuwar hukumar kula da arewa maso gabas, jigogin jam’iyyar APC mai mulki na ‘kara bada tabbacin fara aikin hukumar.

Tsarin hukumar da ya samu karbuwa a majalisar dattawa shine kula da raya tattalin arzikin arewa maso gabas, bayan da Boko Haram ta yi ma yankin illa.

NAIJ.com ta tattaro cewa sakataren jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce yin wannan hukuma ya ‘kara musu kwarin gwiwa kasancewar ana kan hanyar cika alkwaruwan da aka ‘dauka lokacin yakin neman zabe.

‘Dan yankin arewa maso gabas Mohammadu Inuwa Yahaya, ya amince da matsayin inda ya ce sun ganewa idanunsu irin matsalolin da yankin ya shiga, wasu sun rasa gidajensu da iyalensu, wanda yanzu haka wasu mutanen suna zaune cikin kunci a sansanonin ‘yan gudun hijira.

KU KARANTA KUMA: Tsammani abin da wannan makaho ya yi wa ‘yan gudun hijira sama da 500 a jihar Borno (HOTUNA)

A cewar CSP Ado Ibrahim Gabanni Mai Ritaya, hukumar za ta yi nasara ne kawai idan har ta taimakawa matasa su daina bara ko gararanba kan tituna.

Ana sa ran hukumar za ta yi aiki kamar ta kula da Niger-Delta, NDDC. Haka kuma wata hukumar da ta kasa kai labari itace ta kula da jihohi masu samar da lantarki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel