Yadda El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin shugaban kasa - Tinubu

Yadda El-Rufai da Saraki suka hana ni zama mataimakin shugaban kasa - Tinubu

- Bola Tinubu ya bayyana cewa da yanzu ya zama mataimakin Buhari amma Saraki da El-Rufai suka hana

- Babban jigon na APC ya ce basu goyi bayan Musulmi da Musulmi su shugabanci kasar ba

- Ya ce ya gabatar da sunan Osinbajo sannan kuma ya janye don kada a janyo matsala

Asiwaju Bola Tinubu wanda ya kasance shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-Rufai da kuma shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, sun ki amincewa da kasancewarsa a matsayin mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Majalisar wakilai ta ba yan sanda sa’oi 24 su dawo da takardun kasafin kudi

Ana ta samun cece-kuce na cewa tsohon gwamnan jihar Lagas zai kasance abokin takaran shugaban kasa Muhammadu Buhari har sai lokacin da aka bayyana Farfesa Yemi Osinbajo a wannan matsayin.

Wannan tonon sililin na kunshe ne a cikin wani litaffi mai taken ‘Against the Run of Play,’ wanda shugaban sashin tantance rubutu na ThisDay, Olusegun Adeniyi ya rubuta, jaridar The Punch ta ruwaito.

Tinubu ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party wadanda suka koma jam’iyyar APC kafin zaben 2015 sunyi sharhin cewa Kiristoci daga Arewa bazasu jefa kuri’a ga dan takara Musulmi-Musulmi sannan kuma wannan na iya jefa nasarar jam’iyyar cikin wani mawuyacin hali.

KU KARANTA KUMA: Ba'a mutunta hakkin mallakar Fina-finai a Najeriya - Rikadawa

Jigon na APC ya kuma bayyana cewa El-Rufai ya sanya sunayen Fasto Tunde Bakare na Latter Rain a cikin wadanda zasu zamo mataimakin shugaba Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan bidiyo na NAIJ.com na nuna alama 5 da ya nuna za ka iya samu ciwon zuciya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel