Gwamnan Bauchi zai gina katafaren dakin taro mai mutane 5,000 a sansanin masu bautar kasa

Gwamnan Bauchi zai gina katafaren dakin taro mai mutane 5,000 a sansanin masu bautar kasa

- Gwamnan jihar Bauchi, Barista M. A Abubakar ya yi alkawarin gina wata katafaren dakin taro mai mutane 5,000 a sansanin masu bautar kasa dake Wailo

- Abubakar ya tabbatar da walwala ga duk jami'in bautar kasa da aka tura jihar Bauchi tare da kare lafiyarsu

- Gwamnan ya ce ta hanyoyin aka ne ake iya samun kyakkyawar fahimta tsakanin matasa

A kokarin sa na ganin kowane dan bautar kasa da aka turo jihar Bauchi ya samu isasshen kulawa, gwamna Barista M. A Abubakar ya bada umarnin gina katafaren dakin taro a sansanin masu bautar kasar dake garin Wailo.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu yayin taron masu bautar kasar da aka gudanar na wannan shekarar a jihar.

Gwamnan ya kuma yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da walwala ga duk wani jami'in bautar kasa da aka tura jihar Bauchi tare da kare lafiyarsa a yayin yi wa kasa hidima. Ya kuma kara da cewa sansanin yi wa kasa hidima wata hanya ce ta hada kan al'umma.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labara cewa gwamnan ya kuma ja hankalin masu bautar kasar cewa ta irin wadannan hanyoyin ne ake samun kyakkyawar fahimta tsakanin matasa har ta kai ga an gina kasa.

KU KARANTA KUMA: Caccakar Buhari da Dangiwa Umar yake yi bai kamata ba – Fadar Shugaban kasa

Idan za a iya tunawa gwamnatin Bauchi karkashin Barista M. A Abubakar daga shekarar 2015 zuwa yanzu, ta samar da ingantaccen tsaro a sansanin masu bautar kasar dake Wailo ta hanyar katange musu wajen kwana guda 4 da kuma dakin girkinsu wanda hakan ya jawo masu bautar kasar sun dawo da atisayensu zuwa Bauchi bayan tsawon shekaru da suka dauka suna gudanarwa a jihar Filato.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali wasu 'yan mata masu bautar kasa yadda suke shakatawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel