Binciken rashawa a fadar gwamnati ya dau zafi sosai yanzu

Binciken rashawa a fadar gwamnati ya dau zafi sosai yanzu

- Kwamitin binciken manyan jami'an gwamnatin tarrayar Najeriya biyu da ake zargi da cin hanci ta tabbatar da cewa babu gudu ba kuma ja da baya a kokari na tabbatar da gaskiya komai dacin ta

- Abubakar Malami, ya ce sun gana da dama suna kuma nazari mai fadi da nufin tabbatar da laifi ko kuma akasi

- Ana sa ran cewa kwamitin a karkashin mataimakin shugaban kasa zai mika rahotonsa a cikin tsakiyar makon gobe

A yayin da aka shiga mako na biyu na binciken manyan jami'an gwamnatin tarrayar Najeriya biyu, kwamitin binciken ya ce babu gudu ba kuma ja da baya a kokari na tabbatar da gaskiya komai dacin ta.

Babu dai zato ba kuma tsammani yakin cin hanci da rashawa a tarrayar Najeriya ya karkato zuwa ga bangaren zartarwar kasar inda sakataren gwamnatin kasa Babachir David Lawal da babban jami'in hukumar leke na asiri Ambassada Ayo Oke suka kare tare da fuskantar bincike bayan dakatar dasu a bakin aiki.

An dai fada mako na biyu kuma na karshe a binciken tare da gwamnatin kasar tana fadin an yi nisa sannan kuma babu gudu babu jada baya a yakin.

NAIJ.com ta ruwaito cewa ministan shari'ar kasar kuma dan kwamitin binciken na jami'an biyu, Abubakar Malami, ya ce sun gana da dama suna kuma nazari mai fadi da nufin tabbatar da laifi ko kuma akasi.

Binciken rashawa a fadar gwamnati ya dau zafi sosai yanzu

Fadar gwamnatin tarayya da ke birnin Abuja

Sakamako na binciken 'yan kwamitin dai zai kafa dan ba ta tabbatar da sahihancin yakin da ya kalli kama da dama a cikin alkalai dama masu takama da yin dokoki na kasar. To sai dai kuma akwai tsoron yiwuwar a kwata cikin karatun da ya kalli wanke sakataren a bangare na gwamnatin kasar can baya. Abin kuma da a cewar ministan ke zaman daban a karatun da ya wanke Babachir Lawal can baya da kuma wanda yake shirin ya gudana a yanzu.

Wani rahoton majalisar dattawa da ta ambato dakataccen sakataren da bada kwangila ga kamfanonin da yake da alaka da su, da kuma amincewar babban jami'i na leken asirin na mallakar wasu tsabar kudi har naira miliyan 15,000 dai na zaman ummul aba'isin kafa kwamitin a karkashin mataimakin shugaban kasar da kuma ake sa ran mika rahotonsa a cikin tsakiyar makon gobe.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga Jonathan

A fadar ministan, 'yan kwamitin da ya kai ga titsiye jami'an guda biyu da ragowar wasu da ake kallon na da alaka da batu na kudade, na samun gagarumin ci gaba a kokarin kaiwa ga bankado zahirin al'amari a badakalar da ke nuna irin jan aikin dake gaban kasar. Abin jira a gani dai na zaman sakamako na rahoton da ma tasirinsa cikin yakin dake kara nuna alamun haske ga kasar da ta yi nisa cikin dagwalon na hanci yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel