Kiristoci sun taya yan shi'a jimamin ci gaba da tsare El-Zakzaky

Kiristoci sun taya yan shi'a jimamin ci gaba da tsare El-Zakzaky

- A ranar Laraba ne gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suka hada mabiya addinan Musulunci da Kiristanci suka gudanar da wata zanga zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja

- Sun yi ne domin kara tunatar da gwamnatin tarayya hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke, inda ta bukaci a sake Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenatuddeen daga inda ake cigaba da tsare su

Wannan shi ne jerin gwano na hadin gwiwa da gamayyar kungiyoyin suka shirya a karo na biyu, wanda aka fara gudanarwa daga bakin ofishin sakatariyya gmamnatin tarayya dake Abuja zuwa majalisar kasa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa masu jerin gwanon sun rika tafiya ne suna rera wakokin neman 'yanci ga jagoran na kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Nijeriya, IMN, tare da daga tutoci masu dauke da rubutun Free Zakzaky, wasu kuma suna rike da fastocin hotunan jagoran kungiyar da matarsa.

Kiristoci sun taya yan shi'a jimamin ci gaba da tsare Zakzaky

Kiristoci sun taya yan shi'a jimamin ci gaba da tsare Zakzaky

KU KARANTA: Kunji irin ta'asar da akayi wa fulani a cikin shekaru 2?

Kamar dai yadda Zuma Times ta ambata, idan za a iya tunawa dai a jiya ne wata babbar kotun ta bayar da umarnin bayar da belin madugun kungiyar awaren nan ta Biafra, Nnamdi Kanu, duk kuwa da zargin da ake masa na cin amanar kasa, inda wasu manazarta ke ganin ya dace gwamnati ta rika girmama umarnin kotu, domin kare 'yancin dan Adam da dimukradiyya, ta hanyar sake El-Zakzaky kamar yadda ake shirin sake Nnamdi Kanu.

Yaya ku ke ganin wannan bukata ta kungiyoyin kare hakkin dan Adam, wacce rawa ya dace gwamnatin tarayya ta taka domin kare mutuncin ta a idon duniya?

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai yan Kwadago ne ke yin zanga-zanga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel