Harkokin tsaro na kara tabarbarewa a arewacin kasar nan inji jami'an tsaro

Harkokin tsaro na kara tabarbarewa a arewacin kasar nan inji jami'an tsaro

- Hukumar tsaro da kare al’umma ta sibil difens reshen jihar Jigawa ta ce ta samu manyan laifuka 144 tsakanin watan janairu zuwa Maris na wannan shekara

- Mai magana da yawun hukumar, Malam Abdullahi Adamu ya sanar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) da ke birnin Dutse

Hukumar tsaro da kare al’umma ta sibil difens reshen jihar Jigawa ta ce ta samu manyan laifuka 144 tsakanin watan janairu zuwa Maris na wannan shekara.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Abdullahi Adamu ya sanar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) da ke birnin Dutse.

Ya ce guda casa’in da tara na laifukan sun shafi na kananan laifuka.

NAIJ.com ta tsinkaye shi yana bayyana cewa manyan laifukan sune na sata da lalata kayayyaki da na balle gidajen da na rub da ciki akan dukiyar al’umma da na sara-suka da yunkurin kisan kai da na cin zarafi da kuma na ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Harkokin tsaro na kara tabarbarewa a arewacin kasar nan inji jami'an tsaro

Harkokin tsaro na kara tabarbarewa a arewacin kasar nan inji jami'an tsaro

KU KARANTA: Magunguna 5 da kanunfari keyi a jikin dan adam

Malam Abdullahi Adamu ya kara da cewa hukumar ta sami nasarar hukunta mutane goma sha hudu da ake zargi da aikata laifuka, yayin da guda ashirin da hudu suke jiran hukunci.

Ya ce sun gabatar da mutane uku da ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyi ga hukumar yaki da masu ta’amali da miyagun kwayoyi domin daukan mataki na gaba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wani mai hazaka ne

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel