Almundahana: Kotu ta sake daga shari’ar Bukola Saraki

Almundahana: Kotu ta sake daga shari’ar Bukola Saraki

- Kotu ta sake daga shari’ar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki

- Saraki na fuskantar shari’a ne a gaban kotun da’ar ma’aikata bisa tuhume-tuhume 18 da suka jibanci rashin bayyana gaskiyar yawan dukiyar da ya mallaka

Kotu ta sake daga shari’ar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai, wanda ke fuskantar kotun da’ar ma’aikata.

Da farko dai, an fara daga shari’ar daga 18 ga watan Afrilu zuwa 25, sai yanzu kuma zuwa 27 ga watan Afrilu, a bisa bukatar masu gabatar da kara.

Saraki na fuskantar shari’a ne a gaban kotun da’ar ma’aikata bisa tuhume-tuhume 18 da suka jibanci rashin bayyana gaskiyar yawan dukiyar da ya mallaka.

Almundahana: Kotu ta sake daga shari’ar Bukola Saraki

Kotu ta sake daga shari’ar Bukola Saraki

NAIJ.com ta tuno cewa an dai fara shari’ar ne cikin watan Satumban 2015, amma ta rika samun tasgaro daga bangaren masu gabatar da kara.

KU KARANTA KUMA: Ba'a mutunta hakkin mallakar Fina-finai a Najeriya - Rikadawa

Jim kadan kafin waccan dagewar ta zuwa ranar 18 ga watan Afrilu, kotun da’ar ma’aikatan ta fitar da sanarwa dake cewa ta dage shari’ar ne bisa bukatar hakan daga masu gabatar da kara.

Shugaban sashen hulda da jama’a na kotun da’ar ma’aikatan Ibrahim Alhassan ya ce lauya mai gabatar da kara Rotimi Jacobs shi ne ya bukaci dagewar, bisa dalilin cewa ba shi da lafiya.

Alhassan ya kara da cewa a karon farko lauyan mai gabatar da kara ya ce mai ba da shaida na hudu ne bai sami zuwa ba, yanzu kuma shi ne da kansa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli mace bakaniken mota.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel