Ministan labaran Najeriya ya yi amai ya lashe

Ministan labaran Najeriya ya yi amai ya lashe

- Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi aiki a gida ranar Laraba, amma ba daga yanzu zai rika aiki daga gida ba

- A cewar sanarwar ministan bai taba cewa nan gaba shugaba Buhari zai rika aiki ne daga gida ba

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi aiki a gida ranar Laraba, amma ba daga yanzu zai rika aiki daga gida ba.

Wata sanarwa da ministan ya fitar ta ambato shi yana cewa wasu kafofin yada labarai sun yi wa bayanin da ya yi, kuskuren fahimta.

A cewar sanarwar ministan bai taba cewa nan gaba shugaba Buhari zai rika aiki ne daga gida ba.

Ministan labaran Najeriya ya yi amai ya lashe

Lai Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi aiki a gida ranar Laraba

Ta ce kanun da wasu kafofin yada labarai suka buga cewa "Daga yanzu Buhari zai rika aiki daga gida" bahaguwar fahimta ce aka yi wa kalamansa a wata tattaunawa da 'yan jarida.

KU KARANTA KUMA: Caccakar Buhari da Dangiwa Umar yake yi bai kamata ba – Fadar Shugaban kasa

Jawabin dai ya tayar da hankulan 'yan Najeriya inda wasu ke bayyana fargaba game da halin da lafiyar shugaba Muhammadu Buhari take ciki.

Sai dai a wani sautin kalaman ministan da aka nada lokacin da yake jawabi ga manema labarai, an jiyo shi yana cewa shugaban kasa zai rika aiki ne daga gida.

Yayin taron 'yan jaridar, Alhaji Lai Mohammed ya ce na tabbata kun lura cewa shugaban kasa ba ya nan.

Ba ya nan ne saboda ya ce a bar shi ya huta, don haka ya bukaci mataimakinsa ya jagoranci taron (Majalisar Zartarwa), in ji shi.

"Kuma zai rika aiki ne daga gida. Ya ce ma a kai masa duk fayel-fayel dinsa zuwa gida."

A cewarsa, mai yiwuwa ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai gana da shugaban kasa nan gaba a yau don tuntuba.

KU KARANTA KUMA: Ba'a mutunta hakkin mallakar Fina-finai a Najeriya - Rikadawa

NAIJ.com ta tuno cewa tun bayan dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga jinyar kwana 50 ne, aka daina ganinsa a bainar jama'a.

Karo uku kenan a jere, shugaban kasar bai halarci taron Majalisar Zartarwar kasar na sati-sati da ya saba jagoranta ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari ya kawo karshen matsalar tattali kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel