“Ba zan manta da Dasuki da El-Zakzaky ba” – inji gwamna Fayose

“Ba zan manta da Dasuki da El-Zakzaky ba” – inji gwamna Fayose

- Gwamna Fayose yayi alkawarin halartan sauraron karar Dasuki da El-Zakzaky

- Fayose yace baya goyon bayan raba Najeriya

Biyo bayan halartan zaman sauraron karar shugaban kungiyar masu karajin samar da kasar Biafra, Nnamdi Kanu da gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose yayi, gwamnan yace zai cigaba da halartan zaman zauraron karar Sambo Dasuki da kuma Ibrahim El-Zakzaky.

Fayose ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na AIT, inda yace dalilin zuwansa kotun shine don tabbatar da adalci ga dukkan kabilun Najeriya.

KU KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama yansandan bogi ɗauke da buhuhunan wiwi a Kano

Gwamnan yace: “Bani da wata alaka da Kanu, amma na dade ina jan hakulan yan Najeriya dangane da keta hukuncin kotu da gwamnatin shugaba Buhari keyi.”

“Ba zan manta da Dasuki da Zakzaky ba” – inji gwamna Fayose

Gwamna Fayose tare da Nnamdi Kanu

Fayose ya cigaba da fadin: “Ni fa mutumin Arewa maso gabas ne, kuma ni mutumin kudu ne, kai ni cikakken dan Najeriya ne, don haka zan halarci zaman karar Dasuki da na Zakzaky. Kotuna da dama sun bada umarnin sakin Dasuki, amma gwamnati tayi kunnen uwar shegu.”

Daga karshe Fayose ya bayyana ma majiyar NAIJ.com cewa gwamnati ce da kanta ta samar da Kanu daukaka sakamakon cigaba da rike shi da take yi.

“Bana goyon bayan raba Najeriya, amma idan mutane suna karajin neman kasa, ku rabu dasu suyi ta yi. Sa’annan gwamanti ta dinga yi ma hukuncin kotu biyayya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon Fayose a kotu yayin da kai ma Nnamdi Kanu ziyara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel