Za’a karrama Sarki Muhammadu Sunusi a jami’ar Amurka dake Yola

Za’a karrama Sarki Muhammadu Sunusi a jami’ar Amurka dake Yola

- Jami'ar Amurka dake jihar Adamawa zata yaye dalibanta

- Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ne babban bako mai jawabi

Daliban jami’ar Amurka dake jihar Adamawa zasu samu karbi bakoncin mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi a ranar bikin kammala karatunsa 13 ga watan Mayu.

Shugaban jami’ar LeGene Quesenberry ne ya sanar da amsa gayyatar Sarkin Kano na halartar taron, don ya gabatar da jawabi ga daliban da sauran mahalarta taron, daga bisani kuma jami’ar zata karrama shi da digirin digirgir.

KU KARANTA: An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

NAIJ.com ta samu bayanai dake nuna bikin kammala karatun na bana zai wakana ne a dakin taro na tunawa da Lamido Aliyu Mustafa, kuma za’a fara sauran shanukan bikin tun a ranar 12 ga watan Mayu.

Za’a karrama Sarki Muhammadu Sunusi a jami’ar Amurka dake Yola

Sarki Muhammadu Sunusi

Sarkin Kano ya kasance tsohon dalibin kwalejin Sarakuna ne dake jihar Legas, daga nan ya haura zuwa jami’ar Ahmadu Bello inda ya karancu sha’anin tsimi da tanadi, sai kuma ya wuce jami’ar kasar Sudan. Sarki yayi aikin banki a bankin First Bank, inda daga nan ya zama shugaban babban bankin Najeriya a shekarar 2009.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarki Sunusi yayi caccaka, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel