Hukumar yansanda tana bincikar wani ɗansanda da yayi barazanar kashe mutane muddin Buhari ya mutu

Hukumar yansanda tana bincikar wani ɗansanda da yayi barazanar kashe mutane muddin Buhari ya mutu

- Hukuamar yansanda ta fara bincikar jami’inta da yayi alwashin kashe mutane 200

- Dansanda Inusa Saidu Biu yayi alkawarin kashe mutane 200 idan shugaba Buhari ya mutu

Jim kadan bayan bayyanar wani rahoto dake nuna wani dansanda mai suna Inusa Saidu Biu ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa sai ya hallaka mutane 200 muddin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu sakamakon rashin lafiyar dake damunsa, sai gashi hukumar yansanda ta sanar da cewa zata fara binciken wannan lamari.

NAIJ.com ta ruwaito a labarin rubutun da Inusa yayi a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook inda yayi wannan barazana.

KU KARANTA: An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

Hukumar yansandan ta sanar da haka ne ta shafin sadarwarta na Tuwita cewa: “Hukumar yansandan Najeriya zata gudanar da bincike akan wani zance da wani jami’inta Inusa Saidu yayi a shafin Facebook. Sanannen abu ne, bai kamata jami’in dansanda ya dinga irin wannan magana ba.”

Hukumar yansanda tana bincikar wani ɗansanda da yayi barazanar kashe mutane muddin Buhari ya mutu

Sanarwar Yansanda

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai shin da gaske shugaba Buhari ya daidaita tattalin arzikin kasa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel