Alhinin cikar El-Zakzaky kwanaki 500 a kurkuku: Babban lauya ya aika ma Buhari wasiƙa

Alhinin cikar El-Zakzaky kwanaki 500 a kurkuku: Babban lauya ya aika ma Buhari wasiƙa

- Shugaban yan shi'an Najeriya Ibrahim El-Zakzaky ya cika kwanaki 500 a daure

- Yan shi'a sun gudanar da zanga zangar lumana a Abuja

Yayin da mabiya addinin shi’a suka gudanar da zanga zangar jimamin cikar malamin su El-Zakzaky da matarsa Zeenatu kwanaki 500 a daure a hannun gwamnati a ranar Laraba 26 ga watan Afrilu, wani babban lauya Femi Falana ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sako malamin.

Babban lauyan ya aika ma shugaba Buhari wannan bukata tasa ne a cikin wata doguwar warka daya aike ma shugaban kasan, inda ya shawarcin shugaba Buhari da yayi ma hukuncin kotuna biyayya ta hanyar sakin Zakzaky.

KU KARANTA: An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

Mabiya Zakzaky sun gabatar da zanga zangar ne a garin Abuja inda suka kai har bakin majalisun dokokin kasar nan don cigaba da yunkurin da suke yin a ganin lallai an saki malamin nasu.

Alhinin cikar Zakzaky kwanaki 500 a kurkuku: Babban lauya ya aika ma Buhari wasiƙa

Falana

Tun a watan Disambar 2015 ne aka kama Zakzaky biyo bayan wani arangama da akayi tsakanin mabiyansa da Sojojin Najeriya, inda aka kashe sama da yan shi’a 347.

NAIJ.com ta ruwaito Falana yana kumfar bakin lallai gwamnati ta saki Zakzaky tunda dai har yanzu bata tuhume shi da aikata wani laifi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shawara: A zauna lafiya inji tsohon soja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel