Kotu ta yanke ma ɓarayin babur hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke ma ɓarayin babur hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Barayin Babur sun gamu da mummunan hukunci daga kotu

- Kotu ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babbar kotun jihar Osun karkashin jagorancin alkaliya mai shari’a Olubunmi Ayoola, ta yanke ma wasu mutane 4 da aka kama da laifin satar babur hukuncin kisa.

Kotun ta kama mutanen hudu ne da laifin satar babur din a akan babban hanyar shiga garin Oshogbo, babban birnin jihar Osun, inji rahoton jaridar Daily Trust.

KU KARANTA: “Buhari ba shi da isashshen lafiya, ya koma gefe ya huta” – Inji Makarfi

Mutanen dun hada da Samuel Job mai shekaru 19, Daniel Abraham mai shekaru 20, Joseph Moses dan shekara 24 sai Gideon Ode dan shekaru 25 da haihuwa, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta shaida mana.

Kotu ta yanke ma ɓarayin babur hukuncin kisa ta hanyar rataya

Barawon babur

Lauya mai kara Idiat Abdulrahman Temitope ta bayyana ma kotu cewar wadanda ake tuhuman sun aikata wannan laifi ne a ranar 14 ga watan Oktoban 2013, a lokacin da suka yi amfani da wuka suka yi ma wani mutum mai suna Abubakar Rauf fashin da makami suka kwace masa babur.

Sai dai lauyan wadanda ake kara Promise Jones ya nemi kotu tayi ma wadanda yake wakilta sassauci.

Amma mai shari’a Olunbunmi Ayoola tayi watsi da bukatar lauyan, inda ta nuna gamsuwa da lauya mai kara, kuma ta yanke ma wadanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan Najeriya yace zai koma sata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel