EFCC ta kama wata mota cike fal da maƙudan kuɗaɗe a Abuja

EFCC ta kama wata mota cike fal da maƙudan kuɗaɗe a Abuja

- Jami'a hukumae EFCC sun kama wata mota dauke da makudan kudade

- EFCC ta kama motar ne a babban birnin tarayya Abuja

Al’ummar unguwar Shendam Close dake saman titin Anthony Anyaoku dake yankin Arewa 11 na babban birnin tarayya Abuja sun fuskanci wata takaddama data kaure yayin hukuma ta kama wata mota dauke da makudan kudi.

Fitaccen tsohon dan jarida dattijo Timawus Mathias ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook inda yace jami’an hukumar EFCC tare da sojoji ne suka tare motoci guda uku dake cike da jakukunan ‘Ghana must go’ da dama cike da kudi.

KU KARANTA: Dangote ya ƙaddamar da kamfanin haɗa manyan motocin Tirela

Motocin kuwa sun hada da Marsandi S350 mai lamba KTG 01 AA da kuma Lexus SUV mai lamba ABC 11 AKK, sai kuma mota kirar BMW 640i, jami’an EFCC da suka kais u 7 da kuma sojoji guda 2 sun tare motocin ne da misalin karfe 4:50 na yammacin ranar Talata 25 ga watan Afrilu.

EFCC ta kama wata mota cike fal da maƙudan kuɗaɗe a Abuja

Jmai'an EFCC

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar mutanen unguwar sun cika da mamaki yayin da aka kama motocin, inda har sai karfe 6 na yamma jami’an EFCC suka waste daga unguwar.

Majiyar ta cigaba da bayyana cewar wani mutumin da aka kama a cikin motar ya bayyana cewar wasu abokansa ne suka bashi motar, amma a yanzu haka sun tsere. Sai dai suma jami’an EFCC basu bayyana wanene mamallakin kudaden ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda ake samun kudi ta hanyar tona barayi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel