Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga Jonathan

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga Jonathan

-Fadar shugaban kasa ta yi jawabi mai girma akan Goodluck Ebele Jonathan

Fadar shugaban ta bakin mai magana da yaun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, ta mayar da martani da tsohon shugaban kasa, GoodLuck Jonathan, akan maganar da yayi na cewa gwamnatin shugaba Buhari ta ma iyalinsa bita da kulli.

Femi Adesina yayi wannan bayani ne ta shafin sada zumuntarsa ta Facebook inda yace:

“Ya zama tilas ga fadar shugaban kasa ta mayar da martani akan labarin da ta karanta a jaridan ranan Laraba, 26 ga watan Afrilu mai take ‘GWAMNATIN BUHARI NA CIN MUTUNCIN IYALINA, FADIN JONATHAN’

Jaridar tace tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi wata tuhuma cikin wani sabon littafin da shugaban majalisar gidan jaridan Thisday, Mr. Olusegun Adeniyi ya rubuta.

Tsohon shugaban kasan ta nuna bacin ransa game da yaddaa gwamnatin shugaba Buhari ke yaki da rashawa.

TOH ! Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga Jonathan

TOH ! Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga Jonathan

Muna son mun bayyana ba tare boye-boye ba cewa shugaba Buhari ba ci mutuncin kowa ba, innama bari yake doka tayi aikinta. Bugu da kari, muna kara jaddada cewa duk wanda bai da kashi a gindi, to ya daina tsoron komai.

Duk wanda ke tsoro to da alaman tambaya akan abubuwan da yayi yana gwamnati. Duk wanda kuma ya ji an zaluncesa, ya garzaya kotu domin neman hakki.

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buhari bai halarci taron FEC ba a yau

Shugaba Buhari yayi imani da dokar kasa kuma dalilin da yasa yaki da rashawansa ke samun nasara kenan.

Akan maganar salon yaki da rashawa shugaba Buhari kuma, wanda tsohon shugaban kasan ya kushe, bisa ga abubuwan da hukumomin yaki da rahsawa bubbugo, ya bayyana fili cewa ashe biri yayi kama da mutum, gwamnatin baya tayi facaka.

Ko yaya na, lokaci zai bayyana mana ta hanyan sakamakon da za’a samu . Shugaba Buhari ba zai canza ra’ayinshi na yaki da rashawa ba sani ba sabo ba.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel