Kotu ta sake daskarar da asusun bankin Patience Jonathan, ta kwace kudinta $5.8m

Kotu ta sake daskarar da asusun bankin Patience Jonathan, ta kwace kudinta $5.8m

- Kotun da ta bada umurnin a saki asusun bankin uwargidan Jonathan ta canza shawaran ta

- Jastis Mojisola Olatoregun ta canza ra’ayinta kan sakin asusun Patience Jonathan na Skye Bank

News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoton cewa uwargidan tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ta yafe kudi $5.8m ga gwamnatin tarayya tilas.

Wannan rahoto ya bayyana cewa Jastis Mojisola Olatoregun na babban kotun tarayya da ke zaune a Legas ranan Laraba, 26 ga watan Afrilu ta bada wani sabon umurnin sadaukar da kudin Mrs Patience Jonathan.

NAIJ.com tana tuna muku cewa jaridar Punch ta bada rahoton ranan Talata cewa hukumar EFCC ta janye bukatar ta bukatan rashin sakin asusun Patience Jonathan na Skye Bank wanda ke kunshe da $15 million.

Kotu ta sake daskarar da asusun bankin Patience Jonathan, ta kwace kudinta $5.8m

Kotu ta sake daskarar da asusun bankin Patience Jonathan

Alkalin hukumar EFCC. Rotimi Oyedepo ya bayyana a kotun da ke Legas inda yace hukumar ta janye karar.

KU KARANTA: Amfanin kanumfari ga jikim dan Adam

Amma a yau Laraba sai zancen ta canza zani, inda kotun ta bada umurni hukumar EFCC ta kwace kudin Patience Jonathan.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel