Yadda Oba na Legas ya 'wulakanta' Ooni na Ife

Yadda Oba na Legas ya 'wulakanta' Ooni na Ife

- Oba na Legas ya ki mika hannu domin gaisa wa da Ooni na Ife a lokacin wani taro a birnin Legas

- Ooni na Ife ya nema gaisawa da Oba na Legas a lokacin da ya shiga dakin taron, amma Oba na Legas kawai ya daga masa hannu

- Wasu ‘yan Najeriya sun yi Allah-wadai da abin da Oba na Legas din ya yi

'Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani a kafafen sada zumunta bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda Oba na Legas ya ki gaisawa da Ooni na Ife a bainar jama'a.

Oba Rilwan Aremu Akiolu, mai shekara 73, ya ki mika hannu domin gaisa wa da Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi, mai shekara 42 a lokacin wani taro a birnin Legas.

A bidiyon da ake yada wa a shafin Twitter, a lokacin da Ooni na Ife ya shiga dakin taro ya mika wa Rilwan hannu don su gaisa amma maimakon hakan, sai kawai ya daga masa hannu ya ki yarda su yi musabaha.

Yadda Oba na Legas ya 'wulakanta' Ooni na Ife

Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi

Bayan Akiolu ya ki mika wa Ogunwusi hannu su gaisa, sai kawai Ooni na Ifen ya juya ya koma inda aka ajiye masa kujerarsa ya zauna.

A kabilar Yarbawa dai ana yi wa Ooni na Ife kallon sarkin sarakuna kuma shi ne gaba da Oba na Legas.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari cewa, an nada Mista Ogunwusi ne a baya-bayan nan, yayin da Akiolu ya shafe dogon lokaci a matsayin Oba na Legas.

KU KARANTA KUMA: Sarkin Kano ya karɓi bakoncin kungiyar JIBWIS ta ƙasa a fadarsa

Jama'a a Twitter dai sun yi Allah-wadai da abin da Oba na Legas din ya yi:

Ugochukwu Azonobi ya ce: "Ya kamata a gaya wa Oba na Legas cewa Ooni tsatson Oduduwa ne kuma ba sa'ansa ba ne".

Yayin da Olajohun Olutumi ya ce: "Ban san abin da ya faru ba, amma koma mene ne, bai kamata Oba na Legas ya yi haka ba. Ya nuna rashin dattaku".

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sariki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC
NAIJ.com
Mailfire view pixel