YANZU YANZU: Majalisar wakilai ta ba yan sanda sa’oi 24 su dawo da takardun kasafin kudi

YANZU YANZU: Majalisar wakilai ta ba yan sanda sa’oi 24 su dawo da takardun kasafin kudi

- Majalisar wakilan Najeriya ta ba yan sanda sa’oi 24 su dawo da dukkan takardun dake da alaka da kasafin kudin 2017

- Majalisar ta kuma yi Allah wadai da kai samame gidan Goje da jami’an tsaro sukayi a ranar 20 ga watan Afrilu

Majalisar wakilan Najeriya ta ba yan sanda sa’oi 24 su dawo da dukkan takardun dake da alaka da kasafin kudin 2017 da ake zargin sun tafi da shi daga gidan sanata Danjuma Goje, wanda ke shugabantar kwamitin kasafin kudi.

Majalisar ta kuma yi Allah wadai da kai farmaki gidan Goje da jami’an tsaro sukayi a ranar 20 ga watan Afrilu.

NAIJ.com ta tuno cewa wasu tawagar jami’ai na musamman daga hedkwatan tsaro, na Abuja sun kai farmaki a gidan Goje, tsohon gwamnan jihar Gombe dake Abuja a ranar 20 ga watan Afrilu.

Rahotanni sun ce sun awangaba da kudade da kuma wasu kayayyaki daga gidan.

Har yanzu hukumar yan sanda bata bayar da dalilin kai samamen ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari ya kawo karshen matsalar tattali kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel