YANZU YANZU: Yan sanda sun dauke takardun kasafin kudin 2017 – Goje ya fada ma majalisar dattawa

YANZU YANZU: Yan sanda sun dauke takardun kasafin kudin 2017 – Goje ya fada ma majalisar dattawa

- Sanata Danjuma Goje ya fada ma majalisar dattawan Najeriya cewa an kaddamar da batan takardun kasafin kudin 2017

- Takardun sun bata ne bayan farmaki da yan sanda suka kai gidan Goje dake Abuja

Sanata Danjuma Goje ya fada ma majalisar dattawan Najeriya cewa an kaddamar da batan takardun kasafin kudin 2017, wanda suka hada da fayil 18, na’ura mai kwakwalwa da wasu abubuwan.

Goje wanda ya ke a matsayin shugaban, kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, ya fada ma yan majalisa masu rinjaye cewa rahoto a kan kasafin na 2017 ya bata ne sakamakon bincike da yan sanda sukayi a gidan san a Abuja a kwanaki.

Da yake magana a kan farmakin sanatan ya ce an tsayar da tsare-tsare a kan kasafin kudin 2017 tunda yan sanda sun kai farmaki gidan sa sannan kuma sun tafi da takardun.

Ya ba majalisar dattawa da yan Najeriya hakuri kan jinkiri da aka samu gurin gabatar da kasafin kudin.

NAIJ.com ta rahoto a baya cewa jami’an hukumar EFCC sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje dake Abuja.

Amma gurin mai da martani, Wilson Uwujaren, kakakin hukumar EFCC ya karyata cewan EFCC keda alhakin kai farmakin.

A yanzu ana zargin Goje, wanda sanata ne a yanzu kan cewa ya aikata rashawa a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar Gombe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A cikin wannan bidiyo na NAIJ.com dake kasa, mataimakin sakataren labarai na APC, Timi Frank, ya yi gargadin cewa jam’iyyar san A iya fadi a zaben 2019.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel