Dangote ya ƙaddamar da kamfanin haɗa manyan motocin Tirela

Dangote ya ƙaddamar da kamfanin haɗa manyan motocin Tirela

- Dangote tare da hadin gwiwar wani kamfani sun kafa kamfanin hada motoci

- Kamfanin zai dinga hada motoci 10,000 a duk shekara

Hamshakin attajirin nan dan Najeriya Aliko Dangote tare da hadin gwiwar kamfanin ‘Sinotruck’ ya kaddamar da kamfanin hada manyan motoci kirar Tirela a Najeriya.

A ranar Talata 25 ga watan Afrilu ne kamfanin ta fitar da rukunin motocin data hada na farko a Najeriya, inda take yin aikin awanni 8, kuma tana hada motoci 5 a kowane rana.

KU KARANTA: Hukumar EFCC tayi caraf da likitan Goodluck, ta tasa ƙeyarsa zuwa kotu

Shugaban kamfanin Mir Hikmat Thapa ya zagaya da manema labaru kamfanin, sa’annan yayi musu jawabi kamar haka:

Dangote ya ƙaddamar da kamfanin haɗa manyan motocin Tirela

Dangote

“Da zarar mun fara aiki na tsawon awanni 24, zamu dinga harhada motoci guda 20 zuwa 30 a kowane rana. A yanzu mun farad a SKD ne, muna jiran sauran sassan jikin motocin CKD su fara isowa kafin mu fara aiki akan su.”

Thapa yace wannan kamfanin hadin gwiwa ne tsakanin Dangote da Sinotruck, inda yace Sinotruck nada kashi 65 na kamfanin, yayin da Dangote keda kashi 35, inji majiyar NAIJ.com.

Thapa yace kamfanin nada daman hada motoci 10,000 a duk shekara, don haka zata kula da bukatun yan Najeriya musamman masu son fitar da motoci. Bugu da kari kamfanin zata samar da ayyuka da yan Najeriya su 3000.

Dangote ya ƙaddamar da kamfanin haɗa manyan motocin Tirela

Motocin Tirela

Thapa yace “An kafa kamfanin Sinotruck ne a shekarar 1960 a kasar Hong Kong, kuma sune kamfani da suka fi fitar da manyan motoci daga China.”

Daga karshe yace “Wannan wata dam ace da zata inganta tare da habbaka tattalin arzikin Najeriya tare da samar ma matasa da dama aikin yi, kuma wannan dama ne ga masu sha’awar hada motoci su fara.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli mace bakaniken mota

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel