Kunji mummunar ta'asar da akayi wa fulani makiyaya a cikin shekaru 2?

Kunji mummunar ta'asar da akayi wa fulani makiyaya a cikin shekaru 2?

- An bayyana cewa Fulani makiyaya sun yi asarar rayukan da ba su kasa ga 600 ba, kuma an sace musu shanu sama da milyan biyu a cikin shekara biyu.

- Sakataren Kungiyar Miyetti Allah na Kasa, Usman Ngelzarma ne ya bayyana haka yau Talata a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai a Jalingo.

Baya ga wadanda aka kashe da kuma wadanda aka sace, ya ce an sha sace da dama ana yin garkuwa da su da nufin a biya kudi kafin a sake su.

Ya ce wannan kashe-kashe, hare-hare da satar shanun da aka rika yi wa Fulani makiyaya, abin ya rika faruwa ne a yankuna da dama cikin kasar nan.

‘‘Amma duk wannan cuta da kisa da ake yi mana, abin takaici wasu bangarorin jaridun kasar nan ba su damu da yayata barnar da ake mana ba.’’

NAIJ.com ta kuma tattaro cewa ya kuma yi tir da saka siyasa da aka yi a batun rikicin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa, sau da yawa a koda yaushe Fulani ake dora wa laifi, ko da kuwa su aka kai wa hari aka karkashe su.

Kunji mummunar ta'asar da akayi wa fulani makiyaya a cikin shekaru 2?

Kunji mummunar ta'asar da akayi wa fulani makiyaya a cikin shekaru 2?

KU KARANTA: An kawo karshen bukin samun zaman lafiya a Adamawa

Ya kafa misalai kuma da yadda ’yan fashi ke yin shiga irin ta Fulani a wasu wurare kamar jihar Binuwai, Enugu, Anambara da Kudancin Kaduna domin su yi fashi, daga baya sai a ce ai Fulani ne. Usman ya ce su na yin shigar ne don su bata sunan Fulani.

Ya yi tsokacin cewa rashin kyakkyawar sadarwa da fahimtar juna akasari ke haddasa rigingimun Fulani da makiyaya.

Ya ce ya je Jihar Taraba ne domin wani taron wayar da kai da fahimtar juna tsakanin Fulani da manoma da aka shirya wa kananan hukumomi 16 na jihar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel