Jami'an tsaro sunyi wa dalibai masu zanga-zanga rubdugu

Jami'an tsaro sunyi wa dalibai masu zanga-zanga rubdugu

- Jami'an tsaro da suka kunshi sojoji da Yan-sanda, gami da DSS da kuma Civil Defense, sun kwantar da zanga-zangar lumana da daliban jiha Kogi suka gudanar a cikin garin Lokoja

- Daliban na zanga-zanga ne bisa dalilin yajin aikin da manyan makarantun gwamnatin jihar ke yi na tsawan sama da wata uku.

Daluban sun yi dafifi a mahadar hanyoyi ta NATACO tun wajen karfe bakwai na safe, wadda ita ce hanya mafi cinkoso a garin Lokoja dake zuwa Lokoja zuwa Abuja.

NAIJ.com sun samu labarin cewa daliban sun rika fadin cewa mun gaji da yajin aikin da makarantun gwamnati suke yi, mun zaunu gida haka nan, daliban 2015/2016 an ja masu rashin shiga cikin rukunin A na masu zuwa bautar kasa a wannan shekarar ba.

Jami'an tsaro sunyi wa dalibai masu zanga-zanga rubdugu

Jami'an tsaro sunyi wa dalibai masu zanga-zanga rubdugu

KU KARANTA: Kasar Amurka ta karrama Dangote da Abdulaziz Yari

Sai dai majiyar mu ta ta rawaito mana cewa jami'an tsaron sun yi amfani da bulalar doki wajen zane masu zangazangar tare da kuma cafke wasu.

Sai dai majiyar ta mu ta tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Mr Williams Ayah, inda ya tabbatar da kama mutum uku cikin masu zangazangar, amma ya ce ba wanda aka ci ma zarafi a yayin kwantar da zangazangar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai masu tada kayar baya ne

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel