Shirin tsige Sarki Sanusi: Saraki da El-rufai sun roki gwamnatin Kano ta sassauta

Shirin tsige Sarki Sanusi: Saraki da El-rufai sun roki gwamnatin Kano ta sassauta

- Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sun shiga sahun masu rarrashin Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje

- Suna yi ne domin ya janye batun dakatar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sun shiga sahun masu rarrashin gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin ya janye batun dakatar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Majiyar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ganduje ya kashe wayoyinsa tare da tsawaita zaman sa a Chana domin kaucewa masu rokonsa akan batun. Sannan kuma Sarkin ya kira wayar Ganduje domin su yi magana ya kasa samun sa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa sannan bugu da kari ya na son bulaguro zuwa kasar ketare amma masarauta ta shawarce shi da ya dakata har sai Ganduje ya dawo an san inda aka dosa.

Shirin tsige Sarki Sanusi: Saraki da El-rufai sun roki gwamnatin Kano ta sassauta

Shirin tsige Sarki Sanusi: Saraki da El-rufai sun roki gwamnatin Kano ta sassauta

KU KARANTA: Wani soja ya bugi farar hula, ya sa shi birgima cikin kwatami

Zuwa yanzu dai an koma kamun kafa wajen mataimakin Gwamna Farfesa Hafizu Abubakar don ya rarrashi Ganduje akan batun.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaro da suka kunshi sojoji da Yan-sanda, gami da DSS da kuma Civil Defense, sun kwantar da zangazangar lumana da daliban jiha Kogi suka gudanar a cikin garin Lokoja, bisa dalilin yajin aikin da manyan makarantun gwamnatin jihar ke yi na tsawan sama da wata uku.

Daluban sun yi dafifi a mahadar hanyoyi ta NATACO tun wajen karfe bakwai na safe, wadda ita ce hanya mafi cinkoso a garin Lokoja dake zuwa Lokoja zuwa Abuja.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Sarkin Kano na zarge shugabannin yankin Arewa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel