“Buhari ba shi da isashshen lafiya, ya koma gefe ya huta” – Inji Makarfi

“Buhari ba shi da isashshen lafiya, ya koma gefe ya huta” – Inji Makarfi

- Jam'iyyar PDP reshen Ahamad Makarfi ta nemi Buhari ya ajiye mulki ya nemi lafiyarsa

- PDP tace shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar hutuwa

Tsagin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Sanata Ahmed Makarfi ta bayyana cewar kamata yayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma gefe ya huta sakamakon rashin lafiyarsa.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne biyo bayan sallamar jami’in kamfanin jaridar Punch mai suna Olalekan Adetayo daga fadar shugaban kasa, wanda PDP take ganin wannan yunkurin taushe aikin jarida ne.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya karɓi bakoncin kungiyar JIBWIS ta ƙasa a fadarsa

A ranar Litinin 23 ga watan AFrilu ne shugaban masu tsaron fadar shugaban kasa Bashir Abubakar ya sallami dna jaridan kan wasu rubuce rubuce da yayi akan shugaban kasa Buhari.

“Buhari ba shi da isashshen lafiya, ya koma gefe ya huta” – Inji Makarfi

Makarfi

NAIJ.com ta jiyo PDP ta bakin Kaakakin ta Dayo Adeyeye tace: “Mun tabbatar shugaban kasa Muhammadu Buharu ba shi da lafiya, kuma a matsayinsa na mutum, kamata yayi ya samu hutu, tare da cigaba da neman lafiyarsa. don haka bamu yi mamakin rashin bayyanar sa a taron majalisar zartarwa ba.

“Don haka muna gargadin gwamnati data daina yunkurin taushe hakkin yan jaridu, saboda jarida wata ginshiki ne na dimukradiya. Don haka muna sukar matakin da shugaban masu tsaron fadart shugaban kasa yayi.”

Daga karshe PDP tace: “Muna yi ma shugaban kasa fatan Alheri, da samun sauki cikin sauri, kuma muna yi mai fatan Allah ya bashi kwarin gwiwar cika alkawurran daya daukan ma yan Najeriya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan Najeriya yace PDP tafi APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel