An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

- Hukumar NDLEA ta kama turawa masu safarar miyagun kwayoyi zuwa Najeriya

- Mutanen da aka kama yan kasar Brazil ne, kuma mace da namiji ne

Jami’an hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA sun cika hannu da wasu yan kasar Brazil su 2 a filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake Legas yayin da suke kokarin shigo da hodar Ibilis.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito turawan masu suna Dias Dos Santos Marcia Cristina da Lima Pereira Erick Diego suna dauke da hodar Ibilis daya kai nauyin kilo 23 a jakunnansu.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya karɓi bakoncin kungiyar JIBWIS ta ƙasa a fadarsa

Kaakakin NDLEA Mista Ofeyoju ya tabbatar da kama yan kasar Brazil din, kuma yace safarar kwayoyi tsakanin Najeriya zuwa Brazil na karuwa a yan kwanakin nan, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

Yan kasar Brazil da aka kama da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

Shima Kwamandan NDLEA na filin jrigin Ahmadu Garba yace sun kama hodar Ibilis din ne yayin da suke gudanar da bincike tun a cikin jirgi, inda suka gano hodar boye a cikin wasu gwangwanayen abinci.

“Muna bude gwangwanayen sai muka tarar da kwayoyi makare a cikinsu.” Inji kwamanda Garba.

An kama yan kasar Brazil da laifin safarar hodar Ibilis zuwa Najeriya

Masu laifin

Kaakakin NDLEA yace sun kammala shirin gurfanar da mutanen gaban kotu. Shima shugaban hukumar NDLEA na kasa Muhammad Mustapha Abdallah ya yaba ma jami’an hukumar dangane da kamen.

“Naji dadin wannan kamen, wannan ya zaman izina ga sauran kasashen duniya su dage wajen yaki da miyagun kwayoyi.” Inji Abdallah.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya yace yunwa zai kashe yan kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel