An kai hari kusa da garin Gwamna Ortom

An kai hari kusa da garin Gwamna Ortom

– Makiyaya sun kai wani mugun hari a Jihar Benuwe

– An kashe mutane 6 yayin da wasu su ka samu rauni

– Ana zargin Makiyaya Fulani da wannan ta’asa

NAIJ.com na samun labari cewa wasu da ake zargin cewa Makiyaya Fulani ne sun kai hari a Jihar Benuwe.

An kai hari ne cikin Karamar Hukumar Guma inda aka kashe mutane har 6.

Haka dai wasu da dama su ka samu rauni.

An kai hari kusa da garin Gwamna Ortom

Gwamna Ortom na Jihar Benuwe

An kai wannan hari ne a Kauyen Kilthe, wanda nan ne asalin Garin Gwamnan Jihar Samuel Ortom. Wanda abin ya gari a gaban sa yace an kashe mutum 6 wasu kuma har yau ba a san inda su ke ba. Wannan abu dai ya saba faruwa musamman cikin dare.

KU KARANTA: Hafsun Sojin Najeriya a Kasar Brazil

An kai hari kusa da garin Gwamna Ortom

Ana yawan zargin Makiyaya da kai hari

Kwanaki dai da Jami’an ‘Yan Sanda su ka yi bincike an samu mafi yawan masu laifin ba Fulani ba ne. An yi nasarar karbe makamai da dama yayin da ake neman wasu ruwa a jallo wanda daga cikin su Fulani daya ne kacal.

Kuna sane cewa Shugaban hafsun Sojin kasar Bangladesh ya kawo wata ziyara Najeriya inda zai yi har kwanaki 5 domin ganin yadda kasar sa za ta taimakawa Najeriya karashe murkushe ‘yan ta’ddan Boko Haram.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

AAn saki jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel