Allah ya yi: Yadda gwamnonin Najeriya na shirin magance cutar zazzabin cizon sauro a kasar

Allah ya yi: Yadda gwamnonin Najeriya na shirin magance cutar zazzabin cizon sauro a kasar

- Gwamnatocin kasar na kan daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro

- Ana dai amfani da hanyoyi daban-daban wajen hana kamuwa da cutar

- Sai dai wajibi ne al'umma sai sun bada gudunmuwa

Yayin da a ranar Talata 25 ga watan Afrilu ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, wasu shugabanni a Najeriya sun danganta karuwar matsalar ga dabi'un jama'a na rashin tsaftace muhallan su.

KU KARANTA: Jama’a sun kama ɗan-yankan kai dauke da kafafu, kai da hannayen mutum

Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul'Aziz Yari Abubakar, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya ce gwamnatocin kasar na kan daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai ya ce wajibi ne al'umma sai sun bada gudunmuwa.

NAIJ.com ya ruwaito cewa, wasu 'yan Najeriyar dai na ganin rashin mayar da hankali daga bangaren shugabanni shi ne ya sa har yanzu aka kasa magance matsalar zazzabin cizon sauro a kasar.

Gwamnatocin kasar na kan daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai wajibi ne al'umma sai sun bada gudunmuwa

Gwamnatocin kasar na kan daukar matakai don magance karuwar zazzabin cizon sauro, sai dai wajibi ne al'umma sai sun bada gudunmuwa

KU KARANTA: Ina Shugaban kasa ya shige: Wannan makon ma Buhari bai halarci taro ba

A cewar hukumar lafiya ta Majalisar Dinikin Duniya, wato WHO, daga shekarar 2001 zuwa yanzu, an samu nasarar hana kamuwa da cutar har sau miliyan 663 a yankin nahiyar Afirka kudu da hamadar Sahara, inda a nan ne ake samun kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar.

Ana dai amfani da hanyoyi daban-daban wajen hana kamuwa da cutar, amma kuma wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani da su din na da matukar hadari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wanna NAIJ.com bidiyo yana gaya maka lokacin da ya kamata ka je gwajin kanjamau

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel