Kasar Amurka ta baiwa Dangote da Gwamna Yari babban matsayi

Kasar Amurka ta baiwa Dangote da Gwamna Yari babban matsayi

-An baiwa Dangote da Yari babban matsayi bisa ga gudunmuwarsu

- Yari ya bada tabbacin cewa zasu cigaba da hada kai da kasar Amurka wajen yaki da cutan Maleriya

Kasar Amurka ta alanta gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, a matsayin jakadin yaki da ciwon zazzabin sauro a Najeriya.

An bashi wannan matsayi ne a Abuja, ranan Litinin, a wata taro da hukumar tallafin kasar Amurka USAID ta shirya a Najeriya.

An baiwa Yari wannan matsayi tare da Alhaji Aliko Dangote a taron tunawa da ciwon zazzabin cizon sauri na duniya bisa ga gudunmuwar da suke badawa wajen yaki da ciwon zazzabin cizon sauro a Najeriya.

Wannan shirin ya faru ne a a ofishin jakadan kasar Amurka a Abuja inda ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewale; da mataimakin jakadan Amurka zuwa Najeriya ya halarta.

Kasar Amurka ta baiwa Dangote da Gwamna Yari babban matsayi

Dangote

Yari yace: “ A matsayin shugabanni a duniya, akwai muhimmin bukata ga gwamnatin Amurka da shugaba Donald Trump wajen taimakawa wasu kasashe, musamman kasashen da ke da alaka a tattalin arzikin Amurka da tallafin cigaba.”

KU KARANTA: Goodluck Jonathan ya bayyana wadanda suka yaudaresa a 2015

Shugaban kungiyar gwamnonin yace kungiyar zata cigaba da hada kai gwamnatin Amurka da kuma wasu kungoyin tallafi wajen yaki da zazzabin cizon sauro.

Kasar Amurka ta baiwa Dangote da Gwamna Yari babban matsayi

Kasar Amurka ta baiwa Dangote da Gwamna Yari babban matsayi

Kwanakin baya, gwamna Yari da sarkin Kano Muhammadu Sanusi sun kasance cikin wata cacan baki.

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel