Anya lafiya kuwa: Shugaba Buhari bai halarci babban taro ba

Anya lafiya kuwa: Shugaba Buhari bai halarci babban taro ba

– Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron yau, Laraba, 26 ga watan Afrilu ba

– Yanzu haka mataimakinshi Osinbajo ke jan ragamar taron

– Makonni uku kenan ba'a ga shugaban kasar ba a taron majalisar sa

Kusan makonni uku kenan ba a ga shugaba Buhari a taron majalisar zartarwa watau FEC da aka saba yi kowane mako ba.

A halin yanzu haka Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke jan ragamar taron da ake yi na yau bayan an jira shugaban kasar shiru.

Wasu daga cikin yan Najeriya suna nuna damuwa bisa lafiyar shugaban Kasar.

Anya lafiya kuwa: Shugaba Buhari bai halarci babban taro ba

Shugaban kasa bai halarci babban taron yau ba

Wancan makon da ya wuce ba ayi taron ba sam, inda shugaban kasar yace lokacin an dawo daga hutun Easter a kurarren lokacin don haka aka bari sai Ministoci sun kintsa tukun ta bakin Malam Garba Shehu.

KU KARANTA: An kori wani Dan jarida don yace Buhari bai da lafiya

Anya lafiya kuwa: Shugaba Buhari bai halarci babban taro ba

Yau ma ba a ga Buhari a taro ba

A makon baya ma dai shugaban kasa bai halarci taron ba inda Mataimakin sa ne ya ja ragamar. Ministan yada labarai yace ba wata matsala ce ta sa hakan ba illa-iyaka shugaban kasar ya ba Farfesa Yemi Osinbajo domin ya cigaba da wasu ayyuka na dabam.

Kwanaki aka kori wani Dan jarida daga Fadar Villa mai suna Olalekan Adetayo bayan ya bayyana cewa shugaban kasar bai lafiya ba kuma a ganin sa sai Ranar Juma'a. A taron na yau dai akwai wanda ta maye gurbin Sakataren Gwamnati Babachir Lawal watau Dr. Habiba Lawal.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari ya kawo karshen matsalar tattali kuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel