Kasar Amurka, Ingila da Faransa suka taimaka wajen kayar da ni – Goodluck Jonathan

Kasar Amurka, Ingila da Faransa suka taimaka wajen kayar da ni – Goodluck Jonathan

- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya daura laifin faduwarsa zabe akan Barack Obama, David Cameron da Francois Hollande

- Jonathan yace wadanda ya dogara da su suka yaudaresa

- Kana kuma yace Attahiru Jega, shugaban INEC ya canza masa gab da zabe

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, yace wasu shugabannin kasar waje ne suka taimakawa shugaba Muhammadu Buhari wajen nasara a zaben 2015.

Jonathan yace tsohon shugaban kasan Amurka, Barack Obama ; tsohon firam ministan Birtaniya, David Cameron; da shugaban kasa Faransa, Francois Hollande ne suka taimakawa Muhammadu Buhari wajen nasara a zaben 2015.

Jonathan ya bayyana hakan ne a wata littafi da shugaban jaridar This Day, Mr. Olusegun Adeniyi, ya wallafa. The Ntion ta bada rahoto.

Kasar Amurka, Ingila da Faransa suka taimaka wajen kayar da ni – Goodluck Jonathan

Goodluck Jonathan

Yace: “ Shugaba Barack Obama da ma’aikatansa sun nuna mini cewa suna son canjin gwamnati kuma sun shirya yin komai domin samun hakan. Kana har kawo jiragen ruwa sukayi sukayi ana gab da yin zaben.

KU KARANTA: An hurawa gwamnatin Najeriya wuta

“Da ina shiri da firam minister David Cameron amma daga bayam na lura cewa Amurka sun shawarceshi ya juya mini baya. Ban san Obama da gaske yake wajen tabbatar da cewa na fadi ba sai lokacin da kasar Faransa ta juya min baya.”

“Amma kwanaki kadan ga zaben, ya hada kai da Amurka wajen goyon bayan abokan adawa.”

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel