Majalisa: Wata Kungiya ta goyi bayan Gwamna El-Rufai

Majalisa: Wata Kungiya ta goyi bayan Gwamna El-Rufai

– Kwanaki Gwamna El-Rufai ya caccaki ‘Yan Majalisun Najeriya

– Gwamnan ya nemi sun bayyana kasafin kudin su

– Yanzu haka wata Kungiya ta goyi bayan wannan magana

NAIJ.com na da labari cewa Kungiyar BudgetIT ta goyi bayan Gwamna Nasur El-Rufai da ya nemi Majalisa ta bayyanawa Najeriya kasafin kudin ta wanda dai har yanzu har su ‘Yan Majalisun ba su sani ba.

Majalisa: Wata Kungiya ta goyi bayan Gwamna El-Rufai

Har yau babu wanda ya san albashin 'Yan Majalisa

Kwanaki Gwamnan Jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufa’i ya caccaki Majalisa wanda har kalaman na sa ba su yi mata dadi ba. Gwamnan yace Majalisa na karbar makudan kudin da ba a san ina ta ke kai su ba. Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ya maidawa Gwamnan martani dai.

KU KARANTA: Za a fara rajistan zabe kwanan nan

Majalisa: Wata Kungiya ta goyi bayan Gwamna El-Rufai

BudgetIT ta goyi bayan Gwamna El-Rufai

Kungiyar BudgetIT mai zaman kan-ta tayi wani taro a Garin Kaduna inda ta kara kira ga Majalisa cewa ta fito da kasafin kudin ta a gani tare da ayyukan da su ke yi. Abiola Sosami ke cewa maganar Gwamna El-Rufai fa tana nan.

Kungiyar ta jaddada kiran da Gwamnan Jihar Kaduna yayi inda tace ba maganar siyasa ba ce kurum don ana bukatar hakan domin kasa ta cigaba. Shugaban Majalisar Dattawar Bukola Saraki dai yayi alkawarin fito da kasafin su a fili amma har yau bai yi hakan ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC na iya shan kasa a zabe inji Dan Jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel