TSA: An yi kira da Gwamnoni su koma amfani da asusu bai-daya

TSA: An yi kira da Gwamnoni su koma amfani da asusu bai-daya

– An yi kira da Gwamnon Najeriya su yi koyi da shugaba Buhari

– Kwararru sun bada shawarar Gwamnoni su rika amfani da TSA

– Hakan zai gyara tattalin arzikin Kasar Inji masana

NAIJ.com na samun labari cewa kwararru a harkar tattalin arziki sun yi kira da Gwamnonin Jihohin Najeriya su yi koyi da Gwamnatin Tarayya wajen dabagga tsarin nan na asusun bai daya watau TSA.

TSA: An yi kira da Gwamnoni su koma amfani da asusu bai-daya

Gwamnatin Buhari ta dabagga tsarin TSA

Daily Trust ta kawo wannan rahoto daga wani taro da aka yi na masana a Abuja wanda ita ta shirya. Farfesa Aminu Mika’il shugaban Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto yayi kira da Gwamnonin kasar su dabbaga tsarin TSA.

KU KARANTA: An samu karuwar lantarki a Najeriya

TSA: An yi kira da Gwamnoni su koma amfani da asusu bai-daya

An yi kira da Gwamnoni su yi koyi da Buhari

TSA din na taimakawa wajen hada asusu zuwa wuri guda wanda wannan zai taimaka wajen sha’anin Gwamnati. An kuma yi kira da Hukumomi irin su Kwastam da FIRS mai kula da haraji su kara kaimi wajen aiki su.

Kwanakin baya Sarkin Kano yace wasu Gwamnonin ba su da aikin yi sai zuwa Kasar China domin su karbo bashi. Mai martaban yace akwai gyara a lamarin kasar. Gwamnan Kaduna kuma yayi kira ga Majalisa ta bayyana kasafin ta a fili.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kasuwa na bayan shugaban kasa Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel