Wutar lantarkin da Najeriya ke samu ya karu

Wutar lantarkin da Najeriya ke samu ya karu

– A halin yanzu wutar lantarkin da Najeriya ke samu ya kara yawa

– Yaznu ana samun fiye da Mega-watt 4500 na lantarki

– Hakan na nuna cewa dai ana samun karuwar wuta a kasar

A jiya NAIJ.com ta kawo labari cewa Ministar kudi ta kasa watau Kemi Adeosun ta bayyana yanzu abin da ke gaban ta shi ne talakan Najeriya ya amfana da Gwamnati. Ministar tace yanzu ta talakawan Najeriya ake kokarin a gani sun samu abin da su ke bukata na rayuwa.

Wutar lantarkin da Najeriya ke samu ya karu

Wutar lantarki na kara samuwa a Najeriya

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tace cikin matsalolin da ake fama da su a Najeriya akwai rashin isassun gidajen zama, da wadataccen abinci da kuma sha’anin tsaro da ma wutar lantarki.

KU KARANTA: An kirkiro sabuwar allurar masassara

Wutar lantarkin da Najeriya ke samu ya karu

Ministan wuta Fashola

Yanzu haka muna samun labari cewa wutar lantarki da Najeriya ke samu ya haura Mega-watta 4500. Wannan dai gagarumin kari aka samu daga abin da ake samu a baya. A wannan shekarar dai har ta kai ana samun mega-watt 4775.

Hakan dai ya taimaka wajen yawan lokutan da ake samun wuta a cikin kasar musamman birane. Jama’a da dama dai sun tabbatar da cewa yanzu su shar maganar wuta don abubuwa suna kama hanya ba kamar da ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An kera wani jirgi a Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel