Jama’a sun kama ɗan-yankan kai dauke da kafafu, kai da hannayen mutum

Jama’a sun kama ɗan-yankan kai dauke da kafafu, kai da hannayen mutum

- An kama wani dan yankan kai a jiha Kwara dauke da kafa da hannayen mutum

- Jama'a sun lakada masa dan banzan duka, kafin yansandan suka kwace shi

A ranar Lahadin data gabata 23 ga watan Afrilu ne mutanen yankin Adewole na jihar Kwara su kayi ram da wani mutumi da suke zargin dan yankan kai ne, bayan sun kama shi dauke da sassan jikin mutum.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar mutumin da aka sakaya sunansa ya sha dukan tsiya a hannun jama’an bayan sun gan shi yana dauke da wasu sassan jikin mutum.

KU KARANTA: Sharuɗa 12 da kotu ta umarci Nnamdi Kanu ya cika kafin samun beli

Sai dai ba tare da jiran jira ba, sai yansandan yakin Adewole suka dunguma zuwa inda ake rikicin, inda suka tarar da barawon cikin jini, nan kuma suka dakatar da dukansa.

Jama’a sun kama ɗan-yankan kai dauke da kafafu, kai da hannayen mutum

Yansanda

Majiyar NAIJ.com ta bayyana mana cewar rikicin ya samo asali ne lokacin da jama’an dake zirga zirga akan hanyar suka fara jin wani mugunyar wari dake fitowa daga wata mota kirar Toyota, wadda ta lalace a yankin.

Hakan ya sanya mutanen unguwar binciken menen a cikin motar, inda suka ci karo da sassan jikin mutum, kafin kace kule, jama’an sun banka ma motar wuta, sa’annan suka diran ma wanda ake zargin.

Kwamishinan yansandan jihar Kwara ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace “Da gaske ne an kama wani mutum dauke da sassan jikin mutane, kuma yaci duka a hannun jama’a. amma mun kama shi, kuma zamu binciki su wanene keda hannu cikin safarar sassan mutanen.”

Majiyar mu ta shaida mana cikin sassan da aka samu tare da mutumin sun hada da kafar mutum guda daya, hannaye biyu da kuma kokon kai, da aka zuba su cikin bakar leda a aka sanya cikin akwatin motar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya ya fusata, kalli abinda yace

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel