Boko Haram: Ka ji kasar da ke shirin taimakon Najeriya

Boko Haram: Ka ji kasar da ke shirin taimakon Najeriya

– Kasar Bangladesh na shirin taimakawa Najeriya wajen yaki da Boko Haram

– Shugaban Hafsun Sojojin kasar ya kawo ziyara Najeriya

– Dama tun can akwai alaka mai kyau a tsakanin kasashen

Shugaban hafsun Sojin kasar Bangladesh ya kawo wata ziyara Najeriya inda zai yi har kwanaki 5 domin ganin yadda kasar sa za ta taimakawa Najeriya karashe murkushe ‘yan ta’ddan Boko Haram.

Boko Haram: Ka ji kasar da ke shirin taimakon Najeriya

Kasar Bangladesh na shirin taimakon Najeriya

Janar Abu Shafiul Huq ya jaddada goyon bayan su da yaki da ‘yan ta’addan da ake yi a Yankin Arewa maso gabashin kasar inda ya tabbatar da cewa su ma za su bada ta su gudumuwar. Janar Shafiul Huq ya bayyana wannan ne a Abuja.

KU KARANTA: Saura kiris a kashe wasu manyan Sojojin Najeriya

Boko Haram: Ka ji kasar da ke shirin taimakon Najeriya

Janar Buratai da Sojojin wata Kasa

Takwarar sa na Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya tarbe sa daga jirgi a Legas, daga nan kuma shugaban Sojin na kasar Bangladesh ya gana da mataimakin shugaban kasa Faarfesa Osinbajo. Akwai doguwar alaka dai tsakanin Najeriya da Bangladesh tun can da.

Kwanaki NAIJ.com ta kawo maku cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana cewa gaskiya fa shekaru 8 ba za su isa a gyara Najeriya. Shugaba Muhammadu Buhari yayi kokari dai wajen murkushe Boko Haram.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya ta kera wani jirgin saman yawo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel