Aikin jarida na fuskantar barazana – Inji CPJ

Aikin jarida na fuskantar barazana – Inji CPJ

- Kungiyar kare hakkin yan jarida ta duniya, CPJ ta ce kafofin yada labarai na fuskantar sabbin barazana na dakile yancin fadin albarakaci

- Kungiyar ta ce gwamnatoci na amfani da dabaru masu sarkakakiya wajen danne harkokin yada labarai

A wani rahoto da ta fitar kungiyar kare hakkin yan jarida ta duniya, CPJ ta ce kafofin yada labarai na fuskantar sabbin barazana na dakile yancin fadin albarakacin baki da kuma tursasawar gwamnatoci.

A rahotonta na shekara shekara wanda aka wallafa a matsayin cikakken littafi da ta yiwa lakabi da hari kan kafofin yada labarai, kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta duniya ta ce gwamnatoci na amfani da dabaru masu sarkakakiya wajen danne harkokin yada labarai da kuma tauye sukar lamirinsu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari cewa, shugaban kungiyar, Joel Simon ya ce matakin wanda ke kara yin kamari babban abin damuwa ne matuka, musamman ya ce batun yada labaran karya da kuma barazana ga yanayin aikin jarida da suka wanzu tun bayan zaben shugaban Amurka Donald Trump.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 8 da za su sa a sake kama Nnamdi Kanu saboda sharaɗi na karbin belin shi

Kungiyar ta yi nuni da cewa kasashe kamar Rasha da China da kuma Mexico suna sauya alkiblar muhawara a shafukan Internet ta amfani da 'yan baranda masu yada farfaganda, yayin da Amurka kuma ke sa ido tare da goge wasu bayanai da sunan yaki da ta'addanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali yadda wani mutum ke zargin dan jaridar NAIJ.com cewa shi ma yana tare da yunwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel