Ma’aikatan banki za su fara tonawa barayi asiri

Ma’aikatan banki za su fara tonawa barayi asiri

– Hukumar EFCC tana samun gagarumar nasara wajen gano kudin da aka sace a Najeriya

– Sabon tsarin gano kudin sata na aiki kwarai a halin yanzu

– An yi kira ga Ma’aikatan banki da su bada hadin kai

Kwanan nan NAIJ.com ta kawo maku rahoton da Ibrahim Magu yake cewa EFCC ta bankado makudan kudi ta sanadiyar sabon tsarin wannan Gwamnatin Tarayya. Sabon tsarin nan na tona-ka-samu-rabon ya taimaka matuka wajen gano kudin da aka sace a kasar nan.

Ma’aikatan banki za su fara tonawa barayi asiri

Shugaban EFCC Ibrahim Magu

Kungiyar ASSBIFI ta manyan Ma’iakatan banki tayi kira ga ‘ya ‘yan ta cewa su bada hadin kai wajen wannan tafiya. Muna samun labari cewa Kwamared Oyinkan Olasanoye ta nemi ‘yan kungiyar su taimakawa wajen tona asirin wadanda suka boye kudin sata a kasar.

KU KARANTA: Dala tayi kasa a kasuwa

Ma’aikatan banki za su fara tonawa barayi asiri

Sabon tsarin gano kudin sata na aiki ainun

Yanzu haka sabon tsarin da aka kawo na tona-ka-samu-rabon-ka ya taimaka wajen gano kudi har N521, 815, 000.000 da kuma Dalar Amurka $53,272,747.000, da Fam na Ingila £122.890.00 da Dalar Euro €547,730.00.

Shugaban kungiyar tayi kira da a hada hannu-da-karfe wajen ganin an yi maganin barayi a kasar. Olasanoye take cewa sai kuma Gwamnati ta dage wajen hukunta wadanda aka samu da laifi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabon tsarin gano kudin sata na aiki ainun

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel