Ina masu bukatar shiga kungiyar magoya bayan shugaba Buhari? - Inji Alh. Nura Abubakar Waziri

Ina masu bukatar shiga kungiyar magoya bayan shugaba Buhari? - Inji Alh. Nura Abubakar Waziri

- Wata sabuwar kungiyar masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari na sanar da fara sayar da fom ga wanda yake da muradin shiga kungiyar

- Kungiyar zata wayar da kan jama’a a kan bambanci sanin dadin mulkin demokradiyya da mulkin soja da sanin hakkin su akan wanda yake wakiltarsu

- kungiyar ta kuma shawarci matasa da su daina dukan 'yan majalisu da kuma farfasa musu motoci

Kungiyar 'Buhari Youth Organisation Ambassador For Change' tana sanar da daukacin masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin jagorancin Alhaji Nura Abubakar Waziri, kungiyar tana sanar da fara sayar da fom ga wanda yake da muradin shiga wannan kungiya akan naira 200 kacal, da kuma kudin rajista naira 300.

Daya daga cikin manufar wannan kungiyar ce bambanci sanin dadin mulkin demokradiyya da mulkin soja da sanin hakkin su akan wanda yake wakiltarsu. Kungiyar Kuma ta yi alwashi cewa lokaci ya yi da talaka zai zabawa kansa mutumen da zasu wakilce shi.

KU KARANTA KUMA: Dole Buhari ya zo neman waraka daga gare ni tun kafin lokaci ya kure – Satguru Maharaji

NAIJ.com ta tattaro cewa, kungiyar ta shawarci matasa da su daina dukan 'yan majalisu da kuma farfasa musu motoci.

Ina masu bukatar shiga kungiyar magoya bayan shugaba Buhari?

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kungiyar ta yi adua cewa: “Allah ya kai mu 2019 yadda suka mana ba daidai ba haka suma za su ga ba daidai ba. Allah ya mana jagora kuma ya sa mu ci jarrabawa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yadda magoya bayar shugaba Buhari ke murnar dawowarsa daga Landon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel