Hukumar zabe ta fara shirye-shiryen yin rijistar zabe a Najeriya

Hukumar zabe ta fara shirye-shiryen yin rijistar zabe a Najeriya

- INEC ta ce zata fara gudanar da rijistar zaben daga ranar Alhamis, 27 ga watan Afirilu, a ofisoshinta da ke a duk fadin Najeriya gaba daya

- Hukumar ta ce zata gudanar da aikin rijistar ne har tsawon watanni 3, sannan za a buga katuttuka a raba

- Hukumar na bukatar matasa wadanda suka cika shekaru 18 da haihuwa da kuma wadanda basu taba yin rijistar ba da su fito su yi registar

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC a jihar Filato ta ce tayi la’akari da kura-kuran da ta fuskanta a lokutan baya wajen yin rijistar masu kada kuri’a da kuma kokarin magance su, don gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2019.

A wani taron ruwa da tsaki a harkar zabe da hukumar ta gudanar don wayar da kan jama’a kan shirin ta na yiwa matasan da suka cika shekaru 18 da haihuwa da kuma wadanda basu taba yin rijistar ba.

KU KARANTA KUMA: Yadda fadar shugaban kasa tayi amai ta lashe

NAIJ.com ta ruwaito cewa, hukumar dai ta ce zata fara gudanar da rijistar zaben ne daga ranar Alhamis, 27 ga watan Afirilu, a ofisoshinta da ke a duk fadin Najeriya, Alhaji Usman Musa Wase, jami’i a hukumar zaben ta ‘kasa ya tabbatar da cewa hukumar zata gudanar da aikin har tsawon watanni 3, sannan za a buga katuttuka a raba.

Wasu da suka sami damar zuwa wannan taron sun bayar da tasu gudunmawar wajen baiwa hukumar shawarwari, don tabbatar da ganin an gudanar da rijistar zabe ba tare da matsala ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel