An kawo karshen bikin samun zaman lafiya a jihar Adamawa (Hotuna)

An kawo karshen bikin samun zaman lafiya a jihar Adamawa (Hotuna)

- Al’ummar yankin Madagali a jihar Adamawa sun kawo karshen bikin nuna murnar dawowar zaman lafiya a yankin su

- Wannan bikin ne karon na farko da al’ummomin yankin ke gudanar domin nuna farin cikinsu game da samun zaman lafiya

- Shugabanin yankin sun yaba rawar da dakarun Najeriya da kuma yan sakai suka taka, na ganin an kawar da ‘yan Boko Haram daga yankin

- Shugaban karamar hukumar Madagali ya yabawa shugaba Buhari da gwamnan jihar bisa wannan nasara

Al’ummar yankin Madagali a jihar Adamawa sun kawo karshen bikin murnar dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin bayan da dakarun Najeriya suka fatattaki mayakan Boko Haram.

Yankin Madagali shine yankin da ya soma fadawa hannun mayakan Boko Haram a jihar Adamawa, kuma wannan ne karon farko da al’ummomin yankin ke gudanar da irin wannan biki na musamman domin nuna farin cikinsu game da samun zaman lafiya, da aka yi a yankin biyo bayan kwato yankin daga ‘yan bindiga masu tada kayar baya da dakarun Najeriya suka yi.

NAIJ.com ta ttataro cewa bikin ya hada da hawan daba, raye-rayen gargajiya da kuma addu’o’i na musamman.

An kawo karshen bikin samun zaman lafiya a jihar Adamawa (Hotuna)

Bikin samun zaman lafiya a yankin Madagali

Da suke gabatar da jawabai sarakuna da shugabanin addini a yankin, sun yaba game da rawar da dakarun Najeriya da kuma yan sakai suka taka, na ganin an kawar da ‘yan Boko Haram daga yankin.

An kawo karshen bikin samun zaman lafiya a jihar Adamawa (Hotuna)

Shugaban karamar hukumar Madagali, Yusuf Mohammad na jawabi a wajen bikin

Tun farko da yake jawabi shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Mohammad, ya ce an shirya bikin ne don nuna farin ciki game da nasarorin da aka samu a yanzu, tare kuma da kawo fahimtar juna a tsakanin al’umomin yankin, biyo bayan abin da wannan tashin hankali ya jawo, inda kuma ya yabawa shugaba Buhari da gwamnan jihar sanata Muhammadu Bindow Umar Jibrilla bisa wannan nasara.

KU KARANTA KUMA: Allah ya isa! Sama da N7tiriliyan zata iya gyara ta'asar da Boko Haram tayi wa Arewa

Wannan biki dai na zuwa ne yayin da akan samu harin sari-ka-noke a wasu yankunan da aka kwaton, batun da ‘dan majalisar wakilai mai wakiltar Michika da Madagali Mista Adamu Kamale ke kira da a ‘kara kaimi.

An dai kamala bukukuwan cikin koshin lafiya duk da yunkurin da wasu ‘yan Boko Haram suka yi na kai hari, yunkurin da dakarun Najeriya suka tarwatsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel