Hukumar NDLEA ta kama yansandan bogi ɗauke da buhuhunan wiwi a Kano

Hukumar NDLEA ta kama yansandan bogi ɗauke da buhuhunan wiwi a Kano

- Hukumar NDLEA ta kama masu safarar wiwi dauke da kilo 715 na wiwi

- Mutanen da aka kama sunyi basaja ne a matsayin yansanda

Hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA ta kama wasu dillalan wiwi a jihar Kano masu safarar kwayoyi a lokacin da suka basaja a zuwan su yansanda ne.

Kwamandan NDLEA reshen jihar Kano Alhaji Hamza Umar ne ya bayyana haka ga manema labaru a ranar Talata 25 ga watan Afrilu cewa sun kama mutanen ne yayin da suke tuka wata mota mai fentin yansanda da suka sanya mata jiniya.

KU KARANTA: Dattijo mai shekaru 87 a rayuwa ya samu ƙaruwa (Hoto)

Umar yace: “Yayin da muka fara bincike akan su, mun gano mutanen daga jihar Edo suke, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Yobe, kuma mun kama su da kilo 715 na tabar wiwi ne, inda ya suka bayyana mana cewar a duk wata suke kai wannan wiwin jihar ta Yobe.”

Hukumar NDLEA ta kama yansandan bogi ɗauke da buhuhunan wiwi a Kano

Jami'an Hukumar NDLEA a bakin aiki

Kwamandan ya kara da cewa: “Da ace sun samu sa’ar wucewa da wiwin nan zuwa jihar Yobe, musamman yadda ake rikcin Boko Haram a wajen, da ba’a san irin barnar da hakan zata haifar ba.”

A wani labarin kuma NAIJ.com ta ruwaito kwamandan NDLEA na Kano yana fadin sun kama wata mota mai lambar Ebonyi dauke da kilo 64 na tabar wiwi da aka sakala a cikin kwalin busashshen kifi, motar kamar yadda kwamandan ya fada tana kan hanyar zuwa Libya ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli matsalar dake tattare da shan lemu kwalba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel