Yadda wani soja ya sanya ɗan saurayi ‘kamo kifin oga’ (Bidiyo/hoto)

Yadda wani soja ya sanya ɗan saurayi ‘kamo kifin oga’ (Bidiyo/hoto)

-Wani Soja ya sanya wani mutum iyo da nutso cikin ruwan datti

-Sai dai menene ya hada su ba, da har ya yanke masa wannan danyen hukunci

Wani faifan bidiyo ya watsu a shafukan sadarwa na zamani na wani jami’in sojan kasa daya tursasa ma wani matashi farar hula iyo a cikin kwatami.

Sai dai ba’a samu gamsashshen bayanin laifin da matashin ya aikata ma sojan ba, da har ya sanya yake masa wannan mummunan hukunci.

KU KARANTA: ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

A cikin bidiyon za’a ga sojan na tsaye a gefe daya yana sa ido akan matashin, yayin da jama’a yan baruwana ke ta tafiya suna harkokin gabansu.

Yadda wani soja ya sanya ɗan saurayi ‘kamo kifin oga’ (Bidiyo/hoto)

Soja da mutuminsa

Bugu da kari sojan na sanye da kayan sarki, yayin da shi kuma sarkin wanka na sanye da kayan atamfa, sai dai NAIJ.com bata samu tabbataccen inda lamarin ya wakana ba.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tsohon soja yace a zauna lafiya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel