Sharuɗa 12 da kotu ta umarci Nnamdi Kanu ya cika kafin samun beli

Sharuɗa 12 da kotu ta umarci Nnamdi Kanu ya cika kafin samun beli

- Babban kotun birnin tarayya ta bada belin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

- Mai shari'a Binta Nyako ta gindaya masa sharudda 12 da zai cika

A ranar Talata 25 ga watan Afrilu ne babbar kotun birnin tarayya Abuja a karkashin mai shari’a Binta Nyako ta bada belin shugaban kungiyar masu karajin samar da kasar Biafara, Nnamdi Kanu saboda rashin lafiya.

Mai shari’a Binta Nyako tace ta gamsu kwarai da gaske Nnamdi Kanu na bukatar a duba lafiyarsa, don haka yana bukatar a duba shi a asibitin kwararru.

KU KARANTA: Daga baya, babban kotun tarayya baiwa Nnamdi Kanu beli

Sai dai mai shari’a Binta Nyako ta zayyana wasu sharudda guda goma sha biyu da lallai sai Nnamdi Kanu ya cika su muddin yana son a bada belinsa, sharuddan sune:

Sharuɗa 12 da kotu ta umarci Nnamdi Kanu ya cika kafin samun beli

Kanu bayan an kammala shari'a

1. Ba zai gudanar da gangami ba

2. Ba zai yi hira da yan jaridu ba

3. Ba zai shiga taron sama da mutane 10 ba

4. Zai kawo wadanda zasu tsaya masa mutane 3, da zasu sauke miliyan 100 kowannensu

5. Daya daga cikin mutanen dole ne ya kasance babban mutum daga kabilar Inyamurai, misalin Sanata

6. Na biyu dole ne ya zamto hamshakin malamin addinin Yahudawa, tunda Kanu yace shi mabiyin addinin Yahudanci ne

7. Na uku kuwa dole ne ya zamto babban mutum mazaunin Abuja kuma yana da kadara a Abuja

8. Dole ne Nnamdi Kanu ya ajiye fasfon sa na Najeriya da hukuma

9. Dole ne Nnamdi Kanu ya ajiye fasfonsa na kasar Birtaniya da kotu

10. Dole ne ya kawo ma kotu rahoton lafiyarsa a duk wata

11. Ba zai taba fita kasar waje ba a wannan lokaci.

12. Daga nan sai mai shari’a Binta Nyako ta dage sauraron karar zuwa ranakun 11 da 12 ga watan Yulio.

Sharuɗa 12 da kotu ta umarci Nnamdi Kanu ya cika kafin samun beli

Fayose tare da Kanu

NAIJ.com ta ruwaito muku cewar gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose tare da tsohon ministan sufurin jiragen sama Osita Chidoka sun halarci zaman sauraron karar a yau.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon belin Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel